Friday 26 January 2024

Labaran Kennywood: Cire Firdausi yahaya a Shirin Labarina yabar baya da kura, Findin mata Dozen zai Shiga kasuwa

SHARE

Firdausi Yahaya (Zainab Labarina) tace da sanin iyayenta ta shiga wannan harkar ta film inda wani Dan uwanta yayi mata hanya, kawo yanzu dai tace a qalla fina Finai 2 kacal kawai tayi Labarina da wani wanda ba'a fara kawo muku shiba.

Firdausi yahaya Sabuwar Jarumar Kannywood  yar asalin jihar Sokoto ta bayyana hakanne a yau cikin shirin da BBC Hausa ta gayyaceta. Inda take nuna jin dadinta yadda a karon farko masoya suka karbeta akan harakar films.

Firdausi dai tace abinda ke sata jin dadi yanzu shine yadda masoyanta ke korafi akan kasheta da akayi acikin labarina wanda hakan yake nuna mata cewa tana da masoya a wannan fagen.

Zaa saki films din mata Dozen a tashar YouTube, haka zalika Shirin RANAR AURENA zaici gaba a ranar 5 ga watan febrairun wannan shekarar.
SHARE

Author: verified_user

0 $type={blogger}: