Tuesday 30 January 2024

Labaran Sokoto: Gwamna Ahmad Aliyu Naci Gaba da Zuba Aiki Badare Ba Rana

SHARE

An ruwaito cewa gwamnan sokoto Ahmad Aliyu Sokoto yana Aiki ba dare ba Rana, Aiki tukuru kamadaga Tattaunawa akan matsalar Tsaro, Aikin gina gari dakuma tattalin arziki.
Ga jawabin mai magana da yawunsa na Kafar Facebook wato Honorable Naseer Bazzah 
"GWAMNA ME AIKIN HAR CIKIN DARE :

A cikin daren nan yanzu, Gwamnan Jihar Sokoto Gwamna Dr. Ahmad Aliyu Sokoto FCNA ya karbi bakunchin wasu muhimman mutane da suka zo daga bangarori daban daban.

A cikin tawagar da Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto yayi zama na musamman dasu akwai wakilai na hukumar Police Service Commission da wakilai na Federal Character Commission da wakilai na PCRC (Police Community Relation Committee) Sokoto Command, da wakilai na Nigeria Police Trust Fund da kuma wakilai na Carriers and Counselling Department, Cabinet Office Sokoto.

Wannan ziyarar tana da nasa ba da aikin Kwamiti na Police Recruitment Board wadanda suka gudanar da aikin tantance matasa masu shiga aikin dan sanda a jihar Sokoto."Agajahub publishers
SHARE

Author: verified_user

0 $type={blogger}: