Tuesday 30 January 2024

Sanatan Sakwkwati ta gabas Ya Kaddamarda Aikin Fanfunan Ruwa Na Zamani Dakuma Rabon Motocin Alfarma Ga Jama'ar yankinsa

SHARE

SANATA LAMIDO YA GIRGIZA SIYASAR GABASCHIN SOKOTO KUMA YA RABA MOTOCHI NA ALFARMA :

Ayau Sanatan Gabaschin Sokoto, Sanata Ibrahim Lamido ya girgiza yankin Gabaschin Sokoto kana ya zazafa siyasar Gabaschin Sokoto da wasu muhimman ayukkan Alhairi wadanda suka kunshi kaddamar da ayukkan samarda ruwan sha na Bohol na zamani da kuma raba manya manyan motochi na Alfarma kirar Honda Accord da Camry ga mutanen Gabaschin Sokoto.

Sanata Lamido ya kaddamar da ayukkan samarda ruwan sha ne wanda zai aiwatar a yankunan Kananan hukumomi 8 da yake wakilta da kuma raba motochin Alfarma masu tarin yawa ga mutanen da suka yimasa wahalar siyasa a zabensa na Sanata.

Muna yabama wannan kokari na Sanata Ibrahim Lamido kuma muna kara jinjinamasa wajen kokarin tunawa da wadanda suka wahala dashi ga siyasa har ya sakamasu da wannan abun Alhairi.


Agajahub publishers
SHARE

Author: verified_user

0 $type={blogger}: