Wednesday 31 January 2024

Labaran Sokoto: Hukumar Harkokin Jinkai ta Bangaren Lafiya Ta Rattaba Hannu kan Yarjejeniyar Aiki da Hukumar Zakkat da Wakafi ta Sokoto

Ayau DG na Sokoto State Contributory Health Care Management Agency (SOCHEMA)  Yusuf Abu Abdulkarim ya jagoranchi hukuma ta SOCHEMA wajen rattaba hannu akan yarjejeniya da hukumar Sokoto State Zakkat and Endowment Commission ( SOZECOM) wadda Malam Lawal Maidoki yake jagoranta.

Wannan hadakar aiki da yarjejeniya zata kawo abubuwan chigaba masu dinbin yawa ga al'ummar jihar Sokoto musamman ga marasa karfi da marasa lafiya. Hakazalika wannan ne karo na farko da aka samu irin wannan hadakar aiki wadda ta kunshi hukumomin guda biyu domin chigaban al'umma.

Agajahub publishers
Labaran Kannywood: Za'a Saki Film Din Darai Web Series

Labaran Kannywood: Za'a Saki Film Din Darai Web Series

Fitaccen Dan film din nan na Kannywood wato Ali Nuhu Muhammad ya bayyana a shafinsa na Facebook ce zasu saki films din Darasi kwanannan.

"Zamu fara kawo muku wannan Sabon Shirin Series din namu mai suna DARASI

Daga Ranar ALHAMIS 15/02/2024

Akan YouTube channel dinmu mai suna
JAKADA HAUSA TV 

DARASI SERIES Shrine da aka shirya domin a fadakar daku kuma a nishadantar daku 

Akwai Darisa da dama a chikin wannan shiri DARASI 

Wanda kamfanin 3SP INTERNATIONAL suna dauki nauyin kawo miki shi.

#DARASI2024
#DARASISERIES
#JAKADAHAUSATVAgajahub publishers
Hotuna: Gwamnan Jahar Zamfara Ya kaddamarda Ma'aikatan Sakai Masu Suna Community Protection Guard (CPG) a Turance

Hotuna: Gwamnan Jahar Zamfara Ya kaddamarda Ma'aikatan Sakai Masu Suna Community Protection Guard (CPG) a Turance

Shirin "yayewa tareda kaddamarda Zamfara State Community Protection Quards (CPG)" dake gudana yanzu haka A Trade fairs Complex, cikin garin Gusau.

Tasamu halartar gwamnonin jaha daban-daban kamar Maigirma Gwamnan jahar Kebbi HE.Comrd.Dr.Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) tare da Gwamnan jahar Sokoto , Gwamnan Jahar Kano Abba Kabir Yusuf suna daga cikin Gwamnoninda suka samu halartar wannam taron tare da sauran wasu Gwamnonin Arewacin Nigeria.

Wannam taron anyishine musamman ga sababbin jami'an tsaron jahar Zamfara domin ƙara Samarda tsaro a jahar dama ƙasarmu nogeria baki ɗaya.
Hakan yafaru a jahar katsina Daga Gwamna Dikko Radda, hakazalika a sokoto inda Dr Ahmad Aliyu ya kaddamar da Yan bangan Sakai a Jahar 

Agajahub publishers
Labaran Sokoto: Gwanatin Dr Ahmad Aliyu Sokoto Naci Gaba Da Aikin Gina Gidaje 500

Labaran Sokoto: Gwanatin Dr Ahmad Aliyu Sokoto Naci Gaba Da Aikin Gina Gidaje 500

Majiyar mu ta Ofishin Sabbin Kafafen Yada Labarai na SSA Ga Gwamnan Jahar Sokoto

Takawo Aiki na 14: Gina Rukunin Gidaje guda 500 akan titin Kalambaina- Wajeke, Wamakko.
Wanda Gwanatin Jahar sokoto takeyi ,

Bayanin Aikin: Gidajen sun ƙunshi gidaje ɗari uku (300) mai dakuna 3 da gidaje ɗari biyu (200) 2.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Mai Girma Gwamna Dr. Ahmad Aliyu Sokoto FCNA ne ya kaddamar da aikin.

Agajahub printers
Sanatan Sakwkwato Ta Gabas Ibrahim Lamido Yasake Yiwa Daliban Yankinsa Gata karanta Cikakken Bayani a Nan

Sanatan Sakwkwato Ta Gabas Ibrahim Lamido Yasake Yiwa Daliban Yankinsa Gata karanta Cikakken Bayani a Nan

Aikin Fanfunan Ruwa Na Zamani Dakuma Rabon Motocin Alfarma Ga Jama'ar yankinsa bai Isa haka ba yanzu sanata Ibrahim Lamido Yasake kaddamar da Shirin bayarda Tallafin Kudi Naira dubu hamsin 50k ga Daliban Yankinsa.
Honorable Naseer Bazzah 
"YANZU HAKA :

Jerin daruruwan dalibai 'yan asalin Gabaschin Sokoto wadanda zasu amfana da tallafin dubu hamsin hamsin daga Sanatan Gabaschin Sokoto, Sanata Ibrahim Lamido a yau din nan."

Gaskiya Sanata Ibrahim Lamido yana kokari sosai.

Agajahub publishers