Wednesday 31 January 2024

Labaran Sokoto: Hukumar Harkokin Jinkai ta Bangaren Lafiya Ta Rattaba Hannu kan Yarjejeniyar Aiki da Hukumar Zakkat da Wakafi ta Sokoto

SHARE

Labaran Sokoto: Hukumar Harkokin Jinkai ta Bangaren Lafiya Ta Rattaba Hannu kan Yarjejeniyar Aiki da Hukumar Zakkat da Wakafi ta Sokoto 

Ayau DG na Sokoto State Contributory Health Care Management Agency (SOCHEMA)  Yusuf Abu Abdulkarim ya jagoranchi hukuma ta SOCHEMA wajen rattaba hannu akan yarjejeniya da hukumar Sokoto State Zakkat and Endowment Commission ( SOZECOM) wadda Malam Lawal Maidoki yake jagoranta.

Wannan hadakar aiki da yarjejeniya zata kawo abubuwan chigaba masu dinbin yawa ga al'ummar jihar Sokoto musamman ga marasa karfi da marasa lafiya. Hakazalika wannan ne karo na farko da aka samu irin wannan hadakar aiki wadda ta kunshi hukumomin guda biyu domin chigaban al'umma.

Agajahub publishers
SHARE

Author: verified_user

0 $type={blogger}: