Sunday 9 February 2020

SIFFAR ALWALAR ANNABI (SAW)

SHARE
SIFFAR ALWALAR ANNABI (SAW) ______________________
✿ Farko yana wanke tafukan hannunsa sau uku, tare da yin niyya. ✿ Sannan sai ya kuskure bakin sa ya shaka ruwa sau uku uku (da kanfata uku) ✿ Sai kuma ya wanke fuskar sa sau uku ✿ Sannan ya wanke hannayensa zuwa gwiwar hannu sau uku, yana farawa da hannun dama ✿ Sai kuma ya shafi kansa da kunnuwansa sau daya ✿ Sannan sai ya wanke kafafuwan sa sau uku, yana farawa da kafan dama. Yana karanta wannan Addu'ar bayan ya gama alwalla; أشهد أن لاإله إلا الله وحده لاشريك له، وأشهد ان محمدا عبده ورسوله، اللهم اجعلني من التوابين واجعلني من المتطهرين" Ash_hadu an-la'ila ha illallahu wahdahu laa sharika lahu, wa ash_anna Muhammadan 'abduhu warasuluhu, Allahumma j alniy minat_tawwabina waj_alni minal mutatahhirina" Fassara: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kad'ai, babu abokin tarayya a gare shi: kuma ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne.Ya Allah ka sanya ni a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni a cikin masu tsarkaka. NB: Ana so duk sanda mutum ya yi alwallah, ya yi sallah raka'a biyu (Ana kiranta NAFILAR ALWALLA). Tsokaci: Ku Sani ya jama'a, ita alwala wata hanya ce ta kankarar zunubai. Amma se ana yinta irin alwallar Annabi (SAW). Allah Ta'ala yasa mu dace.
SHARE

Author: verified_user

0 $type={blogger}: